Header Ads

Canjin kudi: Kotun koli ta tilasta gwamnatin tarayya dakatar da wa'adin 10 ga watan Fabrairu

Ministan Shari'a kuma Babban Lauyan Gwamnatin Nijeriya, Abubakar Malami

Ministan Shari'a kuma Babban Lauyan Gwamnatin Nijeriya, Abubakar Malami, a yayin wata hira da ya yi da gidan talabijin din Arise TV a ranar Alhamis, ya bayyana cewa gwamnati za ta mutunta umarnin da kotun kolin kasar ta bayar a kan karar da wasu gwamnonin jihohi uku suka shigar, inda kotun ta sa a dakatar da aiwatar da wa'adin 10 ga watan Fabrairu na daina amfani da tsofaffin takardun kudi na naira 200, 500 da 1000.

A cikin hirar da aka yi da shi, Ministan ya bayyana cewa ya na fatar idan aka koma sauraron shari'ar, kotun kolin za ta soke wannan umarnin, wato ta bar babban bankin sanya tsarinsa na sanya wa'adin daina amfani da tsofaffin takardun kudin wanda bankin ya sauya.

Ministan ya bayyana cewa gwamnatin ta yanke shawarar bin umarnin kotun kolin ne domin mutunta doka da oda.

A ranar Laraba ne dai kotun kolin ta Nijeriya ta bayar da umarnin dakatar da wa'adin na 10 ga watan Fabrairu har sai zuwa 15 ga watan na Fabrairu lokacin da za ta yanke hukunci a kan karar da gwamnonin jihohin arewacin Nijeriya uku, Kaduna, Zamfara da Kogi, suka shigar suna kalubalantar wa'adin.

No comments

Powered by Blogger.