Header Ads

Canjin kudi: Jihar Ondo ta nemi shiga cikin karar da Zamfara, Kaduna da Kogi suka kai gwamnatin Tarayya kotun koli

Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu

Gwamnatin jihar Ondo ta nemi kotun koli da ta dakatar da gwamnatin tarayya daga shirin ta na sauya fasalin naira da kuma yin wa'adi ga yawan kudaden da kwastomomim banki za su iya cirewa a kullum.

Gwamnatin jihar ta kuma rubuta ta kasance tare da jihohin Kaduna, Zamfara da Kogi a cikin karar da suka shigar a kan dai wannan al'amari.

A cikin karar, wadda aka shigar ranar Alhamis kuma Antoni Janar na jihar Ondo, Charles Titiloye, ya sanyawa hannu, tana neman kotun da ta dakatar da umarnin da gwamnatin tarayya ta bayar ga babban bankin Nijeriya na kayyade yawan kudaden da za a iya cirewa a kullum.

Titiloye ya bayyana cewa wannan shiri ya yi mummunan shafa da tsayar da ayyukan jihar Ondo tsak da kuma shafar hada-hadar tattalin arzuki da kasuwanci a jihar.

Ya dai bayyana cewa kayyade ko nawa za a iya cirewa daga banki take hakkin gwamnatin jihar Ondo ne da na mutanen ta na yin amfani da kudi domin aiwatar da ayyukan cigaba, samar da bashi ga kananan 'yan kasuwanci (wadanda ba su da asusu a banki) kuma haifar da babbar matsala ne ga harkokin kasuwanci a jihar.

Kamar dai yadda bankin ya nuna, mutane za su iya cire naira 500,000 ne kawai a rana yayinda kuma hukumomi ko cibiyoyi za su iya cire naira 5,000,000 a rana. 

Jihar ta bayyana cewa a yayin da ta ke da hukumomi, cibiyoyi da sauran ma'aikatu sama da 149 wadanda ta ke kula da su a kullum a jihar mai mutane sama da miliyan uku, mutanen da ke da asusun banki kasa da dubu dari biyar ne, wadanda za su iya tura kudi kenan.

Ta dai bayyana cewa a halin yanzu, matanen jihar na kwashe awowinsu masu matukar muhimmanci a kan layin ATM domin amsar sabon kudi, su kuma wadanda suke a karkara da sauran kauyuka inda ba banki ko yanar gizo bakidaya ba su da hanyar samu ko tura kudi.

Jihar ta dai nemi kotun da ta duba ta yanke hukunci in tsarin na kayyade kudaden da za a iya cirewa a kullum da kuma irin wahalhalun da mutane ke ciki sakamakon tsarin bai ci karo da sashi na 2 na dokar Money Laundering, sashi na 20,39 da 42 na dokar babban bankin Nijeriya ba.

No comments

Powered by Blogger.