Header Ads

Buhari ya ba da umurnin a ci gaba da amfani da tsohuwar naira 200

Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bai wa babban bankin ƙasar umurnin ya sake fito da tsofaffin takardun naira 200 domin a ci gaba da mu'amala da su a ƙasar.

Shugaban ya bayyana haka ne a cikin jawabin da ya yi wa al'ummar ƙasar da safiyar yau Alhamis.

Buhari, wanda ya ce yana sane da irin halin wahala da al'ummar ƙasar ke ciki, ya ce za a ci gaba da amfani da takardar kuɗin ta naira 200 har zuwa 10 ga watan Afrilu.

Ya kuma buƙaci al'umma da su ƙara haƙuri kan halin da ake ciki.

Ya kuma ce tsofaffin takardun kuɗi na N500 da N1000 ba za a ci gaba da amfani da su ba, amma ana iya kai wa CBN don a canza su.

Jama'a da dama na ganin wannan mataki nasa a mayan yi ba a yi ba, wato hakan ba zai kau da wahalar da jama'a suke ciki na rashin kuɗin ba.

No comments

Powered by Blogger.