Header Ads

Ba za a yi zabe a cibiyoyi 240 ba da ke cikin jihohi 28 har da Abuja - Hukumar INEC

Shugaban INEC 
A yayin da ya rage saura 'yan kwanaki a gudanar da zabe a Nijeriya, hukumar zabe ta kasa wato INEC ta bayyana cewa ba za a gudanar da zabe a cibiyoyin zabe 240 ba da ke cikin jihohi 28 har da babban birnin tarayya Abuja.

Shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, wanda ya bayyana haka a yayin wani taro da jam'iyyun siyasa a Abuja a ranar Litinin, ya bayyana cewa ba wani sabon mai yin rijista wanda yxa yi rijista a wuraren kuma babu mai zabe da ya nuna sha'awar a turasa can mafi yawa saboda dalilin rashin tsaro, domin haka yanzu yawan cibiyoyin da za a gudanar da zabe sune 176,606.

Cibiyoyin da ba za a yi zaben ba, kamar yadda ya bayyana sun hada da cibiya 1 zuwa 12 a jiha hade da Abuja, inda jihohin Imo da Taraba suke da cibiyoyin 34 da kuma 38. 

Da ya ke magana a kan gudanar da kamfe da ake yi, Farfesan kira ya yi, yana mai cewa, "Ina kira ga ciyamomi da shugabannin jam'iyyu da ku kira 'yan takarar ku da magoya bayanku su bi doka. Ina kuma kira ga jami'an tsaro, jami'an leken asiri da sauran hukumomin da ke tabbatar da tsaro a kan su kama, su bincika tare da yin hukunci ga duk wanda aka kama yana tayar da rigima hade da ko yin maganganu wadanda za su tunzura rashin zaman lafiya."

No comments

Powered by Blogger.