Header Ads

Ba shugaban kasar da ya shiryawa mulki sannan ya fara mulkin a Nijeriya - Matthew Kukah

Fada Matthre Hassan Kukah

Shugaban cocin katolika ta Catholic Diocese of Sokoto, Matthew Hassan-Kukah, ya bayyana cewa babu a cikin shugabannin Nijeriya shugaban kasar da ya shirya jagorantar Nijeriya a cikin shekarun ta 62, daga wadanda suka yi mulkin soja har na farar hula. 

Kukah, wanda ya bayyana haka a cikin wata hira da yayi da gidan talabijin din Channels Television a cikin shirinsu na Roadmap 2023 a karshen makon da ya gabata, ya kara da cewa, "Duk ka bi tarihin Nijeriya, ba za ka samu mutum daya da ya fara mulki bayan ya shirya ba."

Kamar yadda shugaban cocin ya bayyana, tun bayan samun 'yan cin kai da Nijeriya ta yi a ranar 1 ga watan Oktobar 1960, an yi shugabannin 16, takwas shugabanni ko Firaministoci na farar hula, guda takwas kuma shugabannin mulkin soja.

Kukah dai a wannan hira ya kamanta dangantakar da ke tsakanin Nijeriya da shugabannin ta na siyasa da aure wanda ke tattare da matsaloli, inda ya ce, "A kodayaushe a matsayina na shugaban coci ina fadawa mutane cewa karo aure ba shine mafitar auren da ke da matsaloli ba. Kamata ya yi a duba menene dalilin matsalar. In kuma aka yi gaggawar karo auren, bayan wani dan lokaci, sai a kasance gara bara da bana.

"To kamar haka ne ma a Nijeriya, mafi yawancin wadannan canje-canje da muke gani ba a shirya ba ake yin su."

Shugaban cocin ya kara da cewa in ka duba a tarihin Nijeriya tun daga shekarar 1960, wadanda suka yi mulkin farar hula shugabannin kasa da firaministoci zuwa wadanda suka yi mulki sakamakon juyin mulki, ba wani abu da za a ce "an fara shi an cigaba da shi."

Kukah ya bayyana cewa Buhari da ke mulki a yanzu a shekarar 2011 ya bayyana cewa ba ya so ya sake zama shugaban kasa ya gaji, amma sai kuma ya dawo nema a shekarar 2015 ya karba mulki daga Jonathan, Jonathan kuma sakamakon abinda ya faru da 'Yar Adua ne ya hau mulki, shi kuwa 'Yar Adua tuni ya ke fadin, "Na gama, ina so in koma jami'a ne in cigaba da koyarwa." Wannan rashin shirin kuwa shine dai daga wanda 'Yar Adua ya gada, Obasanjo.

"Obasanjo yana cikin kurkuku yana fata wata rana ya fito waje, in da hali ya koma gona. Wannan in ka cigaba haka za ka yi ta gani.

"Abdulsalam na gaf da yin ritaya daga soja, Abacha ya rasu shi kuma ya zama shugaban kasa. In muka koma domin duba yadda wannan al'amari ya faru, haka za ka gani."

Dangane da matsalolin da Nijeriya ke fuskanta dangane da samar da abubuwan more rayuwa, shugaban cocin ya bayyana cewa ya kamata ne a yi shugabanci wanda ke duba matsalolin Nijeriya ya kuma shiryawa wadannan matsalolin, inda ya ce, "Rayuwar Nijeriya a nan gaba ta ta'allaka ne ga shugabannin da za su duba cewa ba mu da wutar lantarki me ya sa? Ba mu da hanyoyi me ya sa? Me ya sa abubuwa suka cakude mana? Ba wai ta hanyar gwamnati ba ko siyasa, a'a, ta hanyar komawa baya a yi tunani."

No comments

Powered by Blogger.