Arewa maso gabas na fuskantar babbar matsala a bangaren koyon karatu - Hukumar UNICEF
Hukumar kula da yara ta majalisar dinkin duniya wato UNICEF ta koka da yawan yara wadanda basu zuwa makaranta a arewa maso gabashin Nijeriya, inda ta ce yankin na fuskantar babbar matsala a bangaren koyon karatu kuma uku cikin hudu na yaran da ke zuwa makaranta ba su iya yin karatu ko iya amsa lissafi mai sauki kafin su kai aji shida na firamare.
Shugabar sahen karatu na cikin kasar nan a hukumar, Saadnah Panday-Soobrayan, ce ta bayyana haka a yayin da take jawabi kan kokarin na UNICEF, a yayin tattaunawa da 'yan jaridu wanda hukumar kula da hakkin yara da tattaro bayanai ta ma'aikatar watsa labarai ta kasa ta shirya tare da hadin gwiwar hukumar UNICEF a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
Shugabar ta bayyana cewa hukumar ta majalisar dinkin duniya tare da hadin gwiwar kungiyar hadaka domin taimakon ilimi ta duniya (Global Partnership for Education Accelerated Funding project) wanda taimakon kudi ne na dalar Amurka miliyan 21.5, sun gudanar da horo ga malaman da ba su cancanta ba har mutum 18,000 domin su yi karatu su kuma samu nasara a jarabawar hukumar malamai ta Nijeriya (Teachers Registration Council of Nigeria) a cikin jihohin da suke fama da ayyukan 'yan ta'adda na Borno, Yobe da Adamawa.
A nashi bangaren, shugaban zartarwa na hukumar kula da ilimin firamare da karamar sakandare na jihar Borno, Farfesa Bulama Kagu, ya bayyana cewa faduwar ilimi a kasar nan abu ne sananne domin kuwa wasu ma da suka gama manyan makarantu basu iya karatu da rubutu.
"To amma hakan na nufin ba za mu nade hannu muna kallo ba, dole mu yi tsare-tsare domin ganin an yi gyara a bangaren ilimi. Taimakon hukumar UNICEF da sauran kungiyoyi ana bukatar su sosai."
Shugaban ofishin hukumar ta UNICEF a Maiduguri, Phuon Nguyen, ya bayyana cewa kashi 29 cikin 100 na makarantun da ke yankin ne kawai ke da makarantu da ke da malamai masu matsakaicin shaidar kwarewa.
"Yawan dalubai in an gwada da yawan malamai shine 124:1. Kusan rabin gabadaya makarantun suna bukatar gyara. Kashi 47 cikin 100 ne kawai na makarantun Borno ke da kayan aiki inda jihohin Yobe ke da kashi 32 cikin 100, Adamawa kashi 26 cikin 100.
"A jihar Adamawa, kashi 30 cikin 100 na makarantu ne ke da isassun kayan aiki ga daluban da basu da yawa, kashi 26 a Borno sannan kashi 25 a Yobe.
"Domin haka mamakin kadan ne in kididdigar Multiple Indicator Clusters Survey (MICS 2021) ta ce sama da rabin yara ba sa gama makarantar firamare a arewa maso gabashin Nigeria."
Post a Comment