Header Ads

An yi muzaharar neman a saki fasfo din Shaikh Ibraheem Zakzaky tare da nuna goyon baya ga Falasdinawa a Abuja

Dimbin almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky ne suka fito a yau Laraba da rana domin gudanar da muzaharar neman a saki fasfo mallakin Shehin malamin da na mai dakinsa Malama Zeenah da kuma nuna goyon bayansu ga al'ummar Falasdinawa wadanda haramtacciyar Kasar Isra'ila ke kashewa da ci gaba da mamayewa.

Masu muzaharar, wadanda ke dauke da hoton Shaikh Zakzaky, tutocin Falasdinawa tare da rera wakoki, sun taru ne a Banex Plaza da ke unguwar Wuse II da ke birnin tarayya Abuja, inda suke wakokin la'antar kasar Amurka, sakin fasfo mallakin Shaikh Zakzaky da kuma na nuna goyan baya ga al'ummar Falasdinu.

No comments

Powered by Blogger.