Header Ads

Amurka ta saki 'yan uwan juna 2 bayan shafe shekaru 20 a kurkukun Guantanamo


Abdul Muhammad 

Kasar Amurka ta fito da wasu 'yan uwan juna guda biyu 'yan asalin kasar Pakistan daga kurkukun Guantanamo Bay bayan sun kwashe shekaru 20 ba tare da wata tuhuma ba. 

'Yan uwan guda biyu, Abdul da kuma Mohammed Ahmed Rabbani, Amurka ta kama su ne a kasar Pakistan a shekarar 2002. 

Cibiyar tsaron Amurka, Pentagon, ta ce Abdul Rabbani na da gida wanda ya ke mafaka ga 'yan al-Ka'ida, a yayin da dan uwansa kuma ke shirya masu tafiye-tafiye da kula da kudadensu.

'Yan uwan biyu sun bayyana cewa jami'an leken asira na CIA sun yi masu hora kafin daga bisani a mayar da su kurkukun Guantanamo.

A yanzu haka dai an mayar da su kasar Pakistan.

A shekarar 2002 ne dai shugaban kasar Amurka na lokacin, George W. Bush, ya samar da kurkukun na Guantanamo bayan harin 9/11 da aka kai a birnin New York, wannan waje ma yana a cikin jerin sansanonin sojojin ruwa na kasar Amurka. 

Sai dai sansanin na Guantanamo ya zama wata alama ta ketare iyaka a cikin yaki da ta'addanci, inda wadanda suke kushe al'amarin suka bayyana yananyin horon da ake yi yayin tambayoyi da kuma kulle mutane na tsawon lokaci da ake yi ba tare da shari'a ba.

Shugaban kasar Amurka ya bayyana cewa yana fata ya kulle gidan kurkukun wanda a yanzu haka ya ke dauke da mutane 32. A cikin shekarar 2003, yayin da kurkukun ke yin tashensa, sansanin na dauke ne da mutane 680 a lokacin daya.

"Amurka na jinjinawa kokari da taimakon gwamnatin Pakistan da sauran wadanda ake aiki tare da su wajen kokarin gwamnatin Amurka na rage yawan wadanda ke cikin sansanin da kuma rufe shi daga karshe bakidaya." Kamar yadda ya ke a cikin wani jawabi wanda cibiyar Pentagon ta bayyana.

Jami'an tsaron kasar Pakistan ne suka kama 'yan uwan guda biyu a garin Karachi a cikin watan Satumbar 2002, kuma sun kwashe shekaru biyu a wajen tsare mutane mallakar CIA da ke kasar Afghanistan kafin daga baya a ka mayar da su sansanin na Guantanamo.

A cikin shekarar 2013, Ahmed Rabbani ya fara kauracewa abinci akai-akai, kuma ya cigaba da hakan har na tsawon shekaru bakwai. Ya kan samu ya tsira ne ta hanyar kayan abinci da ke kara lafiya, wani lokacin da karfin tsiya ake sa masa ta hanyar amfani da tiyo.

Wani lauyan wanda ya wakilce 'yan uwan guda biyu, Clive Stafford Smith, ya bayyanawa BBC cewa zai shigar da kara saboda su, "To amma yiwuwar samun diyyarsu kadan ce, haka ma samun ban hakuri." 

An dai yarda ne da a sake su a shekarar 2021, kuma ba a fayyace dalilin kulle su ba.

Matar Ahmed Rabbani na da juna biyo a lokacin da aka kama shi, kuma wata biyar bayan nan ta haihu, bai samu ya gan dan sa ba.

"Na kan yi magana da yaron Ahmed wanda yanzu shekarunsa 20. Mahaifinsa bai taba shafa kansa ba a matsayinsa na mahaifi. Na so a ce ina nan lokacin da suka hadu." Clive Stafford Smith ya bayyana.

Stafford ya kara da cewa da cewa a lokacin da Ahmed Rabbani ke cikin sansanin na Guantanamo an san shi a matsayin babban mai zane-zane, kuma a cikin watan Mayu za a bayyana zane-zanen nasa tare da na wasu masu zane-zanen su 12 kamar yadda Stafford ya bayyana. 

Maya Foa, daraktar justice charity Reprive, wadanda suka samar da taimakon bangaren shari'a ga Ahmed Rabbani, ta bayyana kulewar da aka yi masa da "abu mai cike da hadari" kuma hakan na kara nuni ne da yadda Amurka ta karkace daga tsarin ta na yaki da ta'addanci.


"Sun hana iyali kasancewa da dan su, mai gidansu kuma mahaifi. Wannan rashin adalcin ba za a iya gyara shi ba. Yin cikakken duba cikin irin illar da Guantanamo ta haifar sai an kulle sansanin tukunna." Maya Foa ta bayyana.

No comments

Powered by Blogger.