Header Ads

Amurka na shirin kai hare-hare da makamai masu guba a Ukraine


Laftanar-Janar Igrol

Amurka na shirin kai hare-hare da makamai masu guba a kasar Ukraine ta kuma dora alhakin hakan a kan Moscow, kamar yadda wani babban jami'in soja na kasar Rasha ya bayyana a ranar Talata.

Shugaban sojojin samar da kariya daga nau'o'in nukiliya a kasar Rasha, Laftanar Janar Igrol Kirillov, wanda ya bayyana hakan, ya ruwaito wasu kalamai daga tsohon ambasadan kasar Amurka a Rasha, John Sullivan, wanda ke bayyana cewa sojojin Rasha "sun shiryawa amfani da makamai masu guba a yayin yaki."

Sullivan ya yi kalaman ne yayin wani taro a satin da ya gabata wanda wata kungiya mai zaman kanta ta shirya a kan yakin na kasar Ukraine.

"Muna kallon wadannan kalamai a matsayin abinda Amurka ta yi niyyar yi, ita da wadanda suke laifi tare, su yi amfani da makamai masu guba." Igrol ya bayyana.

Ya dai yi gargadin cewa Rasha za ta binciko tare da hukunta duk wani wanda ke da yunkuri na haifar da amfani da makamai masu guba daga bangaren Amurka, inda ya ce suna fatar cewa in aka yi amfani da makamai masu guba ba za a yi bincike kwakkwara ba saboda yaki, sai a dora laifin kan Rasha.

"A tunaninsu, tunda yaki ake yi, duniya ba za ta yi cikakken binciken waye ke da alhaki ba, a dalilin hakan wadanda suka haifar da al'amarin sai su dora laifin kan Rasha." Kwamandan ya bayyana. 

Kamar yadda babban jami'in ya ce, a farkon watan nan wani jirgin kasa ya kawo wasu kayayyaki masu dauke da guba a birnin Kramatorsk da ke yankin da Ukraine ke iko da shi na Donbas hade da wasu kwalaye guda takwas wadanda ke dauke da alamun "BZ" a jikinsu da kuma alamun hatsarin sinadarai a jikinsu.

BZ wani sinadarin soja ne mara kamshi mai daci wanda ke hana mutum iya yin komai kuma yana iya kasancewa a cikin iska na tsawon makonni uku kuma ya dade a cikin kasa da ruwa da kuma saman mafi yawan abubuwa.

Laftanar Igrol, wanda ya bayyana cewa kayan da aka kawo din a motocin Amurka aka loda su suka tafi domin su hadu da wurin yin amfani da su, ya ce,"Tabbataccen abu shine ana kawo kayayyakin gubar da kuma kayan kariya daga gareta a lokaci daya, wannan na nuna mana cewa ana shirin yin amfani da gubar BZ din sosai a yayin yakin (a cikin kasar Ukraine)." Ya bayyana.

No comments

Powered by Blogger.