Header Ads

Akwai yiwuwar Isra'ila ta kai hari kan ayarin jiragen ruwa na kayan agaji daga Iran zuwa Siriya - Wani rahoto

Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu

Wani babban jami'in soja wanda ba a bayyana sunansa ba na Isra'ila ya shaidawa wata kafar sadarwa ta kasar Saudiyya cewa Tel Aviv ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen jefa bam kan ayarin jiragen ruwan Iran masu dauke da kayan agaji zuwa kasar Siriya wadda ta gamu da ibtila'in girgizar kasa.

A yayin da ya ke magana da Elaph online newspaper, jami'in ya yi ikirarin cewa Iran "na so ta yi amfani da wannan hali da ake ciki" domin aikawa da makami da sauran kayayyaki ga kungiyar nan da ke Lebanon ta Hezbollah.

Kasar Iran ta kasance daya daga cikin kasashen da suke a gaba wajen kai kayan agaji ga kasar Siriya tun bayan da wata girgizar kasa mai karfin 7.8 ta yi barna mai yawa ga yankin arewa maso yammacin kasar.

Jami'in wanda ba a bayyana sunansa ba, ya ce Isra'ila na da "bayanan sirri" domin goyon bayan ikirarin, domin Isra'ila "Ta kara tsananta sa ido a kan duk abinda Iran ke kaiwa Siriya ta ruwa, kasa da sama." 

Wannan barazanar ta Isra'ila na zuwa ne sati biyu bayan jiragen sama marasa matuki (drones) na kasar Isra'ila sun yi yunkurin kai hare-hare a kan motocin kasar Iran sama da dozin biyu masu dauke da kayan abinci daga kasar Iraki zuwa Siriya.

Akai-akai dama Isra'ilan tana kai hare-hare a wurare da dama a cikin kasar Siriya amma ba ta cika yin magana a kansu ba.

Ko a cikin watan Disamba, shugaban sojojin kasar a lokacin, Aviv Kochavi, ya tabbatar da cewa kasar ta Isra'ila ce ke da alhakin wajen yunkurin kai hare-hare a cikin watan Nuwambar shekarar 2022 a kan ayarin da ya yi dakon mai na kasar Iran wanda ya nufi kasar Lebanun kusa da bodar Siriya da Iraki. Wannan hari ne kan manyan tankokin kasar Iran guda 22 da suka kwaso man Iran bayan sun shigo Siriya daga Iraki. 

A kan wannan al'amari, Siriya ta shigar da koke ga majalisar dinkin duniya da sauran manyan zauruka na duniya.

No comments

Powered by Blogger.