Header Ads

Afghanistan ta yi bikin taya Iran murnar cika shekaru 44 da yin juyin-juya hali na Musulunci

Jami'an gwamnatin Afghanistan a wajen bukin

An gudanar da biki a babban birnin Afghanistan, Kabul, domin taya kasar Iran murna da cika shekaru 44 da yin juyin-juya hali na musulunci, wannan biki kuwa ya samu halartar jami'an gwamnatin mai mulki ta Taliban da jami'an diflomasiyya masu wakiltar kasashe daban-daban.

A yayin gudanar da bikin, Shir Mohammad Abbas Stanikzai, mataimakin ministan harkokin kasashen waje na gwamnatin Taliban, ya bayyana cewa juyin-juya hali na kasar Iran tafiya ce domin musulunci kuma abu ne wanda ya ke sananne.

Kuma juyin-juya hali na kasar Iran wani abu ne da ya ke da tasiri a kan sauran kasashe, musamman wadanda ake cutarwa, wannan ya ba su fata cewa su mike tsaye domin yakar zalunci.

Ba da dadewa ba bayan juyin-juya halin kasar ta Iran, tarayyar Sobiya ta kutso cikin Afghanistan. A cikin wadancan shekarun, juyin-juya halin kasar Iran ya ba mutane fata na mikewa tsaye domin tunkarar masu kutsen.

Shekaru arba'in da hudu bayan yin juyin-juya hali na musulunci a Iran, kasashe masu yin bikin tunawa da shi suna ta karuwa tare da kuma ruhin mikewa tsaye domin tunkarar zalunci.

Juyin-juya hali na musulunci da aka yi a Iran ya ba mutane fata na su yaki masu kutsen kuma daga karshe sun kora masu kutsen waje.

No comments

Powered by Blogger.