Header Ads

Abin da ya sa kotu ta tura Murja Kunya Gidan Maza, maimakon gun Hisba

A yau ne kotun shari'a da ke Filin Hoki a Kano ƙarƙashin mai shari'a Abdullahi Halliru ta aike da 'Ƴar TikTok ɗin nan Murja Ibrahim Kunya zuwa gidan yari.

Tunda farko Lauyan Murja, Barrister Yasir Musa ya nemi a tura ta zuwa gun  Hisbah ne maimakon gidan Yari, amma Kotun ba ta amince ba.
Murja a kotu

Lauya Barrister Lamiɗo Abba Soron Ɗinki ne ya karanto mata ƙunshin tuhume-tuhumen da ake mata wadanda ta musanta.

Ana zargin Murja da ɓata suna da barazana ga A'isha Najamu ta Izzar So da kuma Ashiru Idris, wadanda dukannin su abokananta ne.

Haka kuma tuhuma ta biyu ita ce wadda wani lauya Barrista Ali Hamza ya gabatar inda aka zarge ta da yaɗa kalamai na batsa da shiga ta batsa da yunƙurin tayar da hankalin al'ummar jihar Kano.

Kotun ta ɗage sauraron ƙarar zuwa 16 ga watan Fabrairun da muke ciki.


No comments

Powered by Blogger.