Header Ads

Zaɓen 2023: INEC ta ja kunnen ma'aikatan ta kada su riƙa karɓar cuwa-cuwa wurin raba katin rajistar zaɓe

A ƙoƙarin ta na bin ƙa'idoji da kiyaye doka, Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta gargaɗi dukkan ma'aikatan ta da ke aikin raba katin shaidar rajistar zaɓe cewa su guji neman na goro daga hannun masu zuwa karɓar katin shaidar rajistar zaɓe (PVC).

Shugaban Sashen Wayar da Kan Jama'a na INEC a Jihar Abiya ne, Bamidele Oyetunji ya yi wannan gargaɗi a wata tattaunawa da manema labarai a Abiya.

Ya ce babban laifi ne da ka iya kai mutum zaman kurkuku idan aka kama shi ya na neman na goro daga hannun masu zuwa karɓar katin rajistar zaɓe, musamman waɗanda ke da matsalar ganin na su katin a sauƙaƙe.

Wannan gargaɗi ya zo ne bayan wasu mata sun fito sun yi ƙorafin cewa wasu ma'aikata sun nemi su biya su ɗan na goro.

A wani labarin kuma, INEC ta bayyana cewa ta yi haɗin guiwa da  hukumomin EFCC da ICPC domin kamawa da gurfanar da duk wanda aka kama ya na saye ko sayar da ƙuri'u.

Ko cikin watan jiya sai da INEC ta ƙara jaddada cewa "yan siyasa ne ke maguɗin zaɓe ba mu ba".

Yayin da ya rage saura kwanaki 60 a yi zaɓen shugaban ƙasa, a ci gaba da shirye-shirye da ta ke yi, Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta haddada cewa ba ta yin katsalandan wajen shiga harƙallar murɗe zaɓe.

Da ta ke jawabi yayin ganawa da manema labarai da ƙungiyoyin kare haƙƙi, Kwamishanar INEC ta Tarayya da ke Jihar Ebonyi, Onyeka Ugochi, ta bayyana cewa 'yan siyasa ne ke shirya maguɗin zaɓe ba hukumar zaɓe ba.

Ugochi ta ce, "amma da ya ke a wannan zaɓe mai zuwa INEC ta fito da tsauraran matakan hana maguɗin zaɓe kwata-kwata, musamman ta hanyar amfani da na'urar tantance katin ɗan takara, wato BVAS da sauran matakai, babu yadda za a yi 'yan siyasa su ci kasuwar maguɗin zaɓe.

Daga nan ta yi kira ga kafafen yaɗa labarai da ƙungiyoyin kare haƙƙi su tashi tsaye sosai wajen taya INEC tabbatar da ganin cewa 'yan siyasa ba su samu wata kafar yin maguɗi ba, komai ƙanƙantar ta.

"Za mu yi dukkan abin da doka ta tanadar da abin da ya wajaba domin mu kauce wa masu so mu haɗa baki da su. Saboda hakan ba zai yiwu mu bada kai borin 'yan siyasa ya hau ba.

"Kafafen yaɗa labarai da ƙungiyoyin kare haƙƙi ku tashi tsaye a matsayin ku na masu ruwa da tsaki a harkar zaɓe, ku taya INEC tabbatar da ganin an gudanar da sahihin zaɓe a ƙasar nan. Ku taimaka wajen tabbatar da cewa mun yi abin da doka ta wajibta mana mu yi. Kuma ku taimaka wajen hana masu maguɗi su aikata maguɗi."

Daga nan ta sake jan kunne da gargaɗin cewa masu ƙoƙarin sayen ƙuri'u su sani duk wanda aka kama, to zai yi zaman gidan kurkuku na shekara ɗaya.

Haka kuma INEC ta ce ta haɗa kai da hukumomin EFCC da ICPC domin yin maganin kangararrun 'yan siyasar da za su yi ƙoƙarin sayen ƙuri'u a lokutan zaɓe.

Yau dai saura kwanaki 32 a yi zaɓen shugaban ƙasa.

No comments

Powered by Blogger.