Header Ads

Allah ya yi wa Sarkin Dutse, Nuhu Muhammad Sunusi rasuwa

Allah ya yi wa Sarkin Dutse, Nuhu Muhammad Sunusi rasuwa a yau Talata 31 ga watan Janairun shekarar 2023.

Sarkin ya rasu ne a babban birnin tarayya Abuja sakamakon rashin lafiya.

Marigayin, wanda kwamishinan ayyuka na musamman a jihar ta Jigawa, Auwal Danladi Sankara ya tabbatar da rasuwarsa ga BBC, ya rasu ne yana da shekaru 79 a duniya kuma ya taba zama uba ga jami'ar jihar Sokoto a lokacin rayuwarsa.

Sakatare na musamman ga marigayin, Wada Alhaji, ya bayyana cewa ana sa ran yin jana'izar sarkin a gobe Laraba a babban birnin jihar ta Jigawa wato Dutse.

No comments

Powered by Blogger.