Header Ads

Ƙungiyar 'Yan Jarida ta Nijeriya ta karrama mawallafin Blueprint, Mohammed Malagi

Ana karrama mawallafin Blueprint da Manhaja, Alhaji Mohammed Idris Malagi (na 4 daga dama)

Ƙungiyar 'Yan Jarida ta Nijeriya (NUJ) ta ba Shugaban kamfanin buga jaridun Blueprint da Manhaja, Alhaji Mohammed Idris Malagi, babbar kyautar karramawa  ta ɗaya daga cikin manyan masu tallafa wa cigaban aikin jarida a ƙasar nan. A turance, sunan kyautar 'Milestone Recognition Media Icons in Nigeria'.

An yi wa Malagi da wasu hamshaƙan 'yan Nijeriya karramawar ne a wani gagarumin biki da aka yi ran Alhamis a Cibiyar MUSON da ke Legas.

Wasu waɗanda aka karrama sun haɗa da shugaban NUJ na ƙasa,  Cif Chris Isiguzo, da Gwamnan Jihar Legas,  Mista Babajide Sanwo-Olu, da Sufeto-Janar na 'Yan Sandan Nijeriya, Alhaji Usman AIkali Baba, da tsohon gwamnan Jihar Ogun, Cif Segun Osoba, da Ciyaman ɗin jaridun Vanguard, Mista Sam Amuka Pemu, da tsohon gwamnan Jihar Abiya kuma mamallakin jaridun Daily Sun, Sanata Orji Uzor Kalu, da Ciyaman na jaridun Thisday, Mista Nduka Obaigbena, da Ciyaman na kamfanin Daar Communication masu gidajen rediyo da talbijin na AIT da Raypower, Cif Raymond Dokpesi.

Wasu da su ma aka karrama su sun haɗa da Ciyaman na tashar talbijin ta Channels, Mista John Momoh, da tsohon babban editan mujallar The News, Mista Bayo Onanuga, da Ciyaman kuma jagoran kamfanin Media Trust masu jaridun Daily Trust da Aminiya, Malam Kabiru Yusuf, da Manajan Daraktan Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN), Mista Buki Ponle, da Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kano, Alhaji Muhammad Garba, da Editan jaridar Champion na farko, Mista Emma Agu, da tsohuwar janar-manajar labarai ta gidajen rediyo da talbijin na AIT da Raypower, Madam Olufunke Fadugba, da Manajan-Daraktar  jaridar The Point, Dakta Yemi Kolapo da mawallafin jaridar The Marketing Edge, Mista John Ajayi.

Shugaban ƙungiyar ta NUJ, Cif Chris Isiguzo, ya yi bayanin cewa karramawar da aka yi wa Malagi an yi ta ne saboda ganin ya tsaya ƙyam da ƙafafun sa wajen ciyar da aikin jarida gaba a tsawon shekaru, wanda ya tabbatar da cewa shi da sauran waɗanda aka karrama ɗin sun yi aiki tuƙuru wajen tabbatar da wanzuwar 'yancin 'yan jarida, wanda wani ginshiƙi ne na kafuwar mulkin dimokiraɗiyya a faɗin duniya. 

Ya ce yaƙin da waɗannan masu tallafa wa 'yancin aikin jarida ke yi ya na taimakawa wajen habaka dimokiraɗiyyar ƙasar nan wajen tabbatar da gaskiya a gudanar da mulki, tsare gaskiya, bin doka da oda da kuma bai wa kowa damar ya shiga a dama da shi a fagen lamurran jama'a da kuma siyasa.

Isiguzo ya ƙara da cewa: “Ya na su samu walwala, ya wanzar da yanayin aiki tare da kuma zurfafa dimokiraɗiyya ta hanyar ba kowa da kowa dama a yanayi na 'yanci, zaman lumana da samun cigaba a alƙiblar da ake so a fuskanta.

“Waɗannan mutanen da mu ke karramawa a yau sun nuna jajircewa ta wannan fuskar kuma mu na yaba masu saboda hakan. Ya kamata a lura da cewa muhimmancin 'yancin aikin jarida a wajen gudanar da mulki mai nagarta da habaka dimokiraɗiyya da aikin gina ƙasa ba abin wasa ba ne.

"Sai dai kuma, duk da yake ana ganin alfanun aikin jarida, 'yan jarida da dama a Nijeriya su na ci gaba da fuskantar tsangwama da barazana da lahanta masu jiki da ake yi a lokacin da su ke gudanar da aikin su na halaliyar su.

“Irin bajinta da sadaukarwar waɗannan 'yan jarida ya sa mu ke karrama su a yau a karo na farko na karramawar 'Milestone Recognition of Media Icons'. Don haka ne mu ke so mu riƙa yin wannan taron a kai a kai.

"An shirya wannan taro ne domin a karrama tare da nuna girmamawa ga wasu daga cikin waɗannan gwarzaye domin a ƙarfafa wa sauran 'yan jarida gwiwa, sannan a ƙarfafa aikin jarida mai nagarta, da 'yancin aikin jarida da kuma ingantaccen mulki a Nijeriya.”

Shugaban taron kuma tsohon gwamnan Jihar Ogun, Aremo Olusegun Osoba, ya yi kira ga ƙungiyar ta NUJ da ta tashi tsaye ta magance yawaitar kafafen yaɗa labarai na intanet da ake samu waɗanda ya ce su na bata sunan aikin.

Osoba ya yi kira ga NUJ da ta samar da wani gidan yana inda za ta yi wa dukkan 'yan jaridar da ake aiki a Nijeriya rajista.

Alhaji Mohammed Idris Malagi, wato mawallafin Blueprint da Manhaja, wanda kuma shi ne Kakaaki Nupe, har ila yau ɗan siyasa ne a Jihar Neja inda ya yi takarar zama gwamna a jam'iyyar APC a zaɓen fidda gwani da aka yi a watannin baya. 

Ya samu rakiya zuwa taron karramawar a Legas ta 'yan'uwa da abokan arziki. Sun haɗa da tsohon mataimakin gwamnan Jihar Neja kuma tsohon Jakaden Nijeriya a Afrika ta Kudu, Alhaji Ahmed Musa Ibeto; da Shugaban APC na Jihar Neja, Honourable Haliru Zakari, da tsohon ɗan Majalisar Wakilai, Honourable Ibrahim Ebbo.

Waɗansu 'yan rakiyar sun haɗa da babban ɗan kasuwar nan mai harkar inshora, Alhaji Abdulmalik Abubakar Muye, da Babban Kwamishina a Hukumar Sauraren Ƙararrakin Jama'a, Barista Bala Marka, da wani wanda ya yi takarar zama gwamnan Neja a bana, Alhaji Aliyu Idris Rugga, da kuma Sakataren APC na Jihar Neja, Khaleel Ibrahim Aliyu.

Sauran su ne tsohon Shugaban Ƙaramar Hukumar Magama ta Jihar Neja, Honourable AIhassan Ibeto, da Ma'ajin APC na jiha, Dakta Idris Mohammed Gbangba, da Shugaban Matasan APC na jiha, Comrade Abdullahi Suleiman, da zaɓabben Shugaban Ƙaramar Hukumar Lavun ta Jihar Neja, Honourable Isah Kutigi, da dattijo a APC kuma babban ɗan kasuwar nan, Honourable Theo Mamman, da Alhaji Umar Mohammed Wara da fitaccen ɗan APC a Jihar Neja, Honourable Ndagi Lavun.


Malagi (na 1 daga hagu) tare da wasu manya da aka karrama

Malagi (na 1 a dama) lokacin da Sam Amuka Pemu (l) ya ke gaisawa da Cif Segun Osoba

No comments

Powered by Blogger.