Header Ads

Tsohon Kwamishinan Addini ya ce Gwamnatin Ganduje makaryaciya ce

Gwamnan jihar Kano, Ganduje

Tsohon Kwamishinan harkokin addinai na jihar Kano, Dr. Muhammad Tahar Adam (Baba Impossible) ya ce gwamnatin jihar Kano ta Ganduje makaryaciya ce, don kuwa shi ya ajiye mukaminsa, ba korar sa aka yi ba.

Cikin wata tattaunawa da ya yi da manema labarai, Dr Muhammad Tahar ya ce, tun a ranar 30 ga watan Disamba ya kai wa sakataren gwamnati takardarsa ta ajiye aiki, kuma aka karba aka buga sitamfi aka ba shi nasa kwafin.

Cikin takardar dai (Baba Impossible) ya ce bai bayyana dalilinsa na barin aikin ba.

Baba Impossible ya ce shi ma a soshiyal mediya ya ga takarda na yawo wai an kore shi.

Ya kuma ce da shi suke in dai karya za su rika gaya wa jama'a a kansa, ma'ana akwai tonon silili da ke tafe in duk sassan biyu ba su mai da wukar ba.

Sai dai wata sanarwa da Gwamantin Jihar ta fitar mai dauke da sa hannun kwamishinan yada labaran jihar Malam Muhammad Garba ta ce, Gwamnan Jihar Kano Abdullhai Umar Ganduje ne ya sanar da korar kwamishinan harkokin addini daga mukaminsa.

Kuma tuni aka bayar da sunan Dr. Nazifi Bichi a matsayin wanda zai maye gurbinsa.

Sanarwar ta ce "an kori kwamishinan ne saboda halin rashin da’a da yake nuna wa a matsayinsa na ma’aikacin gwamnati mai rike da mukami.

"An same shi yana gudanar da al’amuran ofishinsa a matsayin sana’a ta kashin kansa, har ma yakan rage kwanakin aiki ga ma’aikatan Ma’aikatar, banda ranakun Laraba da Juma’a."

Kwamishinan ya kara da cewa baya ga gudanar da aiki ba tare da tuntubar juna ba, Baba Impossible ba ya biyayya ga gwamnati.
Baba Impossible 

No comments

Powered by Blogger.