Header Ads

An Yi Muzaharar Tunawa Da Waki'ar Buhari Ta 12/12/2015 A Birnin Zazzau


A jiya Juma'a 9/12/2022  'yan'uwa Musulmi Almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky na birnin Zazzau Zaria, suka gudanar da gagarumar Muzahrar tunawa da Waki'a r Buhari ta 12/12/2015 . 
Idan za a iya tunawa a wannan waki'a ce gamayyar jami'an tsaron Nijeriya karkashin jagorancin shugaba Buhari, suka auka wa  'yan'uwa Musulmi Almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky, suka kashe akalla mutum dubu , kana suka kona wasu da ransu suka bizne wasu , daga bisani suka kwashi wasu suka kai su gidan yarin Kaduna suka tsare. 

Daga karshe suka kama Sayyid Ibraheem Zakzaky ( h ) tàre da mai dakinsa Ummushuhada Malama Zeenah Ibrahim, suka tsare har na tsawon shekaru 6,  duk da ko suna dauke da raunuka a jikinsu.

An fara muzaharar ne a daidai randar Babban Dodo, tsakiyar Birnin Zariya  jim kadan da kammala Sallar Juma'a a Masallacin Fadan Zazzau.

Dimbin 'yan'uwa Musulmi na garin Zariya har ma da  makwabta ne suka samu halarta. Shaikh Abdulhamid Bello Zaria  ne ya jagoranci muzaharar tare da gabatar da jawabin rufewa.

An fara lafiya, an kuma kammala lafiya. Allah ya amshi shahadar Shahidanmu.

No comments

Powered by Blogger.