Header Ads

A Sakkwato An Yi Muzaharar Tunawa Da Ta'addancin Buhari Na Disambar 2015 A Zariya

Almajiran Sheikh Ibraheem Yaqoub Alzakzaky na Sakkwato sun fito domin gudanar da jerin gwanon tunawa da abin da ya faru a ranar 12 ga watan Disamba 2015, ranar da shugaban ƙasa Buhari ya tura rundunonin Sojoji a Zariya gidan Sheikh Zakzaky domin ganin bayansa, da kuma neman gwamnati ta sake  Fasfon Sheikh Zakzaky da ta riƙe ta hana shi fita neman lafiyarsa.

A yayin harin na 12 Disamba Sojoji sun kashe sama da almajiran Sheikh Zakzaky dubu tare da jikkata waɗansu ɗaruruwa, ciki har da Sheikh Zakzaky da iyalansa.

Daga Bilal Nasir Umar Sakkwato

No comments

Powered by Blogger.