Header Ads

A BAUCHI AN TUNA SHEKARU BAKWAI DA TA'ADDNCIN BUHARI A KAN HARKA ISLAMIYYA A ZARIYA

Da safiyar Juma'ar nan ne 9/12/2022 "yan'uwa musulmi almajiran Shaikh ZakzakY na yankin Bauchi suka fito muzahara domin shelantawa tare da tunatar da al'umma irin bakin zaluncin gwamnatin Buhari a kan Shaikh Zakzaky da da'awarsa ta Harka Islamiyya a shekarar 2015.

Muzaharar ta Karade dukkanin manyan titunan birnin Bauchin Yakubu ana shelantawa tare da tunatar da al'umma.

Wakilin "yan'uwa na yankin Bauchi, Shaikh Ahmad Yusuf Yashi ne ya jagoranci muzaharar tare da gabatar da jawabin rufewa.

An Fara lafiya tare da kammalawa lafiya.

Daga Lawal K/madaki.

No comments

Powered by Blogger.