Header Ads

2023: INEC ta lissafa abubuwa biyar da za a yi nazari cikin jerin sunayen masu rajistar zaɓe

Daga Wakilin Mu

A shirye-shiryen ganin ta gudanar da sahihin zaɓe a 2023, Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta bayyana ta yi kira ga jama'a su yi nazarin jerin sunayen waɗanda ta yi wa rajistar zaɓe domin a tantance yaran da ba su kai shekaru 18 a cikin waɗanda su ka yi rajista ba.

Wannan bayani ya fito ne daga bakin Kakakin INEC, Festus Okoye, a wata tattaunawar da aka yi da shi a gidan talbijin na Channels, ranar Litinin.

Ya ce bai yiwuwa a ce babu wasu 'yan kura-kurai a cikin jerin sunayen waɗanda aka yi wa rajista. "Dalili kenan INEC ke fitar da sunayen a liƙa a faɗin ƙasar nan, domin kowa ya je ya tantance.

Okoye ya ce akwai abubuwan dubawa muhimmai guda biyar, waɗanda wajibi ne duk wanda ya yi rajistar shaidar zaɓe, to ya je ya tantance sunan sa.

Bayanai biyar da Okoye ya lissafa, sun haɗa da cewa, ya kamata jama'a su yi wa jerin sunayen rajistar duba na natsuwa, domin su tantance gano yaran da ba su kai shekara 18 ba, domin INEC ta cire su.

Haka kuma, duk wanda ya yi rajista zai je ya duba da kyau domin ya tabbatar an rubuta sunan sa daidai a rajistar.

Abu na gaba kuma a ya bakin Okoye, ya na da kyau duk wanda ya yi rajista, to ya je ya duba ya tabbatar ba a yi kuskure wajen rubuta duk wasu bayanan da su ka shafe shi ba.

Akwai kuma batun cewa duk wanda ya yi rajista zai je ya duba ya tabbatar cewa hoton sa da aka liƙa, sama bai kalli ƙasa ba.

Batu na biyar kuma shi ne kira ga jama'a su duba domin su taya INEC dubawa da nusasshe ta idan har yanzu akwai sunayen waɗanda su ka rigaya su ka mutu.

Okoye ya ce tuni dai a na ta ɓangaren, INEC ta tsame sunayen waɗanda su ka yi rajista sau biyu ko fiye da haka.

Sannan ya ƙara da cewa sun bi sunayen dalla-dalla sun cire waɗanda su yi rajista sau biyu.

No comments

Powered by Blogger.