Header Ads

Ambaliya mai zuwa: Minista Sadiya ta gargaɗi jihohi da ƙananan hukumomi kan aikin kwashe jama'a

Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta faɗakar da gwamnatocin jihohi da na ƙananan hukumomi da ma shugabannin jama'a, musamman a jihohin Anambara, Delta, Kuros Riba, Ribas da Bayelsa, cewa ambaliyar ruwa na nan tafe a cikin makwanni masu zuwa, sannan ta yi kira a gare su da su shirya wa aikin kwashe jama'ar da ke zaune a yankuna da hanyoyin da ruwan ke bi. 

 Ministar ta faɗi haka ne a taron da ta yi da manema labarai a ranar Lahadi a Abuja domin bayyana masu ƙoƙarin da gwamnati ke yi na rage raɗaɗin bala'in ambaliya a ƙasar nan, wanda ta ce babbar matsala ce. 

Hajiya Sadiya ta ce duk da gagarumin ƙoƙarin da ake yi na kauce wa matsalolin ambaliyar wannan shekarar ta 2022 kamar yadda Hukumar Nazarin Yanayi ta Nijeriya ta hango zai faru, gwamnatocin jihohi da dama ba su yi wani shiri dangane da ambaliyar ba, wanda hakan ya jawo babbar asarar rayuka da ɓarnata dukiyoyi. 

Ta ce: “Abin baƙin ciki ne a ce an rasa rayuka sama da 603 ya zuwa yau 16 ga Oktoba, 2022. Jimillar mutum 1,302,589 su ka gudu daga muhallin su, mutum 2,504.095 abin ya shafa baki ɗaya, mutum 2,407 sun ji rauni, jimillar gidaje 82,053 sun rushe baki ɗaya, yayin da guda 121,318 su ka lalace a wasu sassa nasu. 

Hekta 108,392 ta gonaki ta lalace a wasu sassa yayin da hekta 332,327 ta salwanta baki ɗaya, wanda ya haɗa da hanyoyi da yawa da sauran muhimman ababen more rayuwa. “A yayin da mu ke alhinin haɗarin nan mai ban takaici na kifewar kwale-kwale da ya faru a Jihar Anambara da sauran wurare, don Allah mu lura da cewa ba wai gaba ɗaya ba mu san abin da ke faruwa ba ne domin kuwa Hukumomin Nazarin Yanayi su na ta gargaɗin cewa jihohi irin su Anambara, Delta, Kuros Riba, Ribas da Bayelsa su na fuskantar barazanar faɗawa bala'in ambaliya har zuwa ƙarshen Nuwamba. “Mu na kira ga gwamnatocin waɗannan jihohin da ƙananan hukumomi da al'ummomi da su shirya wa kwashe mutanen da ke zaune a wuraren da ambaliya ke bi zuwa wurare masu tudu, su samar da tantuna da kayan agaji, da ruwan sha da kuma kayan magani saboda yiwuwar ɓarkewar annobar cututtuka.” 

Bayan haka, wata babbar tawaga da ma'aikatar ta kafa ya na nan ya na shirin kai wa gwamnonin jihohi ziyara domin ganawa da su kan su ƙara ƙaimi wajen ƙarfafa shirin su na tunkarar matsalar ambaliyar kamar dai yadda aka tsara a Shirin Gaggawa kan Ambaliya na Ƙasa, wato 'National Flood Emergency Preparedness and Response Plan'. 

Ana sa ran masu ruwa da tsaki a lamarin za su yi aikin da aka rataya masu a wuyan su domin hana aukuwar mace-mace saboda ambaliya ko wasu cututtuka da ke da alaƙa da rashin lafiya daga al'amarin wanda ka iya faruwa. Bugu da ƙari, Babban Sakataren ma'aikatar, Dakta Nasir Sani Gwarzo, zai jagoranci wata tawaga zuwa ƙasar Kamaru a watan gobe domin su tattauna da hukumomin ƙasar kan batun buɗe dam ɗin Lagdo jefi-jefi. 

Haka kuma kwanan nan za a aiwatar da Shirin Gaggawa kan Ambaliya na Ƙasa domin a samu daidaito wajen aikin tunkarar matsalar ambaliya, sannan a samar da hanyar gudanar da aikin kula da ambaliya a matakan ƙasa baki ɗaya daga sama har zuwa ƙasa. Bayan haka, kusan dukkan jihohi 36 da Gundumar Birnin Tarayya sun karɓi kayan abinci da waɗanda ba na abinci ba domin rage matsaloli daban-daban na bala'in ambaliyar. Darakta-Janar na Hukumar Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), Alhaji Mustapha Habib Ahmed, shi ne ya bayyana haka a wajen taron da ministar ta yi da manema labarai. 

Ya ce: “Labarin da wasu ke yaɗawa cewa wai ba a ga abin da Gwamnatin Tarayya ta yi a jihohin da ambaliya ta shafa ba ƙarya ne. Mu na nan a kowace jiha ta ƙasar nan. Mun kai kayan agaji a kowace jiha ta ƙasar nan.

 "Kuma mu na gode wa Babban Kwamandan Askarawa kuma Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da mai girma Minista. "Za mu ci gaba da yin ƙoƙarin mu wajen sama wa ƙasar nan agaji." 

Waɗanda su ka halarci taron dai sun haɗa da Babban Sakataren ma'aikatar, Dakta Nasir Sani Gwarzo, da shugabannin hukumomi da daraktocin ma'aikatar. Hoto: Minista Sadiya Umar Farouq ta na gabatar da jawabi ga manema labarai

No comments

Powered by Blogger.