Header Ads

YADDA AKA YI JANA'IZAR ALHAJI SULE BACHIRAWA

Jiya Lahadi 21/08/22 bayan Sallar Isha'i ne Allah ya yi wa Alhaji Sule Musa Bachirawa, Direban Sheikh Muhammad Muhmud Turi rasuwa. 
An yi masa Jana'iza yau Litinin bayan karfe goma na safe. Duk da an yi ruwa da safe, Garin kuma na cida, wannan bai hana yan uwa Maza da Mata suka yi dafifi a wajen jana'izar tasa ba.

Bayan an yi masa Sallah a kofar gidansa wadda Malam Ali Abdurrahman Rimin gado ya jagoranta, an dauke shi zuwa Makabartar Ramin Tifa, Bachirawa wajen da aka binne shi, kamar yadda ya yi Wasiyya. An kuma binne shi ne daf da Shahidan Waki'ar Karfi.

Sharif Yusuf Hamza ne ya yi masa talkini da addu'o'i bayan kammala rufe shi. Dk. Sunusi Abdulkadir, Wakilin 'yan'uwa na Kano kuma ya yi wa yan uwa jawabin bankwana da Alhaji Sule Bachirawa, inda ya ce ba mu san komai a tare da shi ba sai alheri. 

Ya kara da cewa Alhaji Sule mun shaide shi da ya tafiyar da rayuwarsa a gwagwarmayar tabbatar da Addinin Allah a doron Allah. Ya kuma kawo hadisi cewa wanda ya yi kokarin ganin addini ya tabbata, sai mutuwa ta riske shi, to shi ya cimma burinsa.
Bayan an kammala, sauran 'yan'uwa sun karasa wajen Kabarin sun gudanar da tasu addu'ar ta musamman gare shi. 

Ana ci gaba da zaman makoki a kofar Gidansa da yake Bachirawa Kano.

Ana tunawa 'yan'uwa Sallatul Wahsha yau. Sunansa Sulaiman Musa. ALLAH YA GAFARTA MASA ALBARKACIN IMAMU HUSAIN (A.S).

No comments

Powered by Blogger.