Header Ads

NEMAN FITINA: WASU ZAUNA GARI BANZA SUN BANKA WUTA A MUHALLIN 'YAN SHI'A A KANO

Daga Muhammad kabir kano


Wasu zauna gari banza a kano sun banka wuta a Wani muhalli mallakar yan shi'a mabiya malam zakzaky da yammacin jiya juma'a.

Lamarin ya faru ne a unguwar dorayi babba a jiya da yamma wajejen  karfe 1:00 na ranar juma'a inda zauna garin banzan suka haura ginin husainiyyar ta baya suka dira ciki sannan suka shiga cikin dakin ajiyar kaya da littafai na ginin suka sace wasu suka tafi da su sannan suka tattara littafan karatun addini da kur'anai masu tsarki da wasu muhimman kayayyaki masu muhimmanci suka kona tare da saka musu taya wajen konawar.

 Daya daga cikin masu hakki da kula da wurin mai suna malam Tukur ya bayyanawa wakilin mu cewa "tun bayan ginin wurin (husainiyyar) muka fara gabatar da karatuttuka da addu'oi da kuma tarukan mu a wajen amma sai ga shi wasu limamai da suke jagorantar sallar juma'a a unguwar ta dorayi babba suke tunzuro zauna gari banza tare da yin kira a mumbarorin su na hudubar sallar juma'a da su afka mana wai tunda sun kai korafi ga hukumomi amma sun gaza daukar mataki a kan mu".Malama Tukur ya kara da cewa "a bara muna cikin gyaran muhallin sai ga irin wannan yan iskan garin sun zo da muggan makamai suka sassari mutanan mu da yawa tare da yiwa da yawa daga cikin mu muggan raunuka har da karaya sannan suka farfasa mana motoci tare da kona wasu, sai ga shi yanzu kuma sun sake dawowa suka yi mana wannan barnar mai tarin yawa, don haka ma muka kirawo yan jarida muka yi hira da su tare da gayyato yan sanda don ganin barnar da suka yi mana wannan karon, sannan wannan filin da aka yi ginin da cikakkun takardun sa tun daga siya har ginin sa, sannan dokar kasa ta banu yancin gudanar da addinin mu yadda muka fahimta a matsayin mu na yan kasa".Dukkan kokarin mu na jin ta bakin limaman da ake zargi da yin hudubar tunzirawar abin yaci tura bai samu ba, amma dai hukumomin tsaro sun sami labarin harin.

No comments

Powered by Blogger.