Header Ads

'Yan Bindiga Sun Hana Dalibai Karatu A Abuja


A safiyar wannan Litinin, iyaye sun yi dandazo a kwalajin gwamnatin tarayya da ke Kwali a birnin Abuja na Najeriya domin kwashe ‘ya’yansu dalibai daga makarantar biyo bayan wani hari da ‘yan bindiga suka kaddamar a kusa da makarantar.

Daya daga cikin iyayen yaran mai suna Mrs. Babep Peace ta bayyana wa Jaridar Daily Trust cewa, ta yi tattaki ne daga birnin Lagos zuwa Abujan domin tafiya da ‘ya’yanta biyu bayan ta samu kiran wayar tarho daga hukumomin makarantar kan barazanar da yaran ke fuskanta.

A cewarta, da misalin karfe 4 na safiyar jiya Lahadi ne ta samu kiran wayar kuma nan take ta kama hanyar tashar mota domin balaguro zuwa Abujan.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da daliban ke zana jarrabawa, amma a cewar Mrs. Peace, zaman lafiya ya fi zama dan sarki.

A ranar Asabar da daddare ne dai ‘yan bindigar suka kaddamar da farmaki kan kauyen Sheda da ke kusa da kwalejin, lamarin da ya jefa tsoro a zukatan yaran.

‘Yan bindiga da mayakan Boko Haram dai sun sha sace dalibai daga makarantun boko a sassan arewacin Najeriya.

No comments

Powered by Blogger.