Header Ads

Kungiyar Kwadago A Nijeriya NLC Na Gudanar Zanga-Zanga A Fadin Kasar

 


Kungiyar kwadago ta Najeriya ta fara gudanar da zanga-zangar kwana biyu domin nuna goyon bayanta ga kungiyar Malaman Jami'o'in kasar ta ASUU da suka shafe watanni suna yakin aiki

Tuni dai kungiyar kwadagon ta umarci rassanta na jihohin kasar da su shirya gudanar da zanga-zangar kwanaki biyu domin nuna goyon bayansu ga kungiyar ASUU.

Wakilinmu a jihar Kano da ke arewacin Najeriya ya aiko mana da rahoton cewa tuni hadakar kungiyoyin kwadagon suka fito domin fara gudanar zanga-zangar

Kwamarate Ummu Khulsum Adamu daga kungiyar NLC reshen jihar Kano ta shaida wa wakilinmu cewa suna zanga-zangar ne domin yaransu su koma makaranta, ta kara da cewa ''Muna son yaranmu su koma makaranta, saboda muna tsaron kar su zame mana 'yan ta'adda, mun yi ne domin neman gwamnati ta duba bukakunmu''

A makon da ya gabata ne Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin kawo karshen yajin aikin cikin makonni biyu

Tun a ranar Litinin 14 ga watan Fabrairu ne kungiyar malaman jami'o'i ta Najeriya, ASUU, ta tsunduma yajin aikin gargadi ga gwamanatin Najeriya na tsawon wata guda.

Yajin aikin malamai a Najeriya ya fi yin tasiri a kan dalibai wadanda ke tsintar kansu cikin damuwa, dalilin da ya sa wasu ke ganin ya kamata kungiyar ta sauya salon tunkarar rikicinta da gwamnatin kasar ba sai lallai ta hanyar yajin aiki ba.


No comments

Powered by Blogger.