Header Ads

Jawabin Shaikh Zakzaky (H) Yayin Tunawa Da Waki’ar Quds Din 2014 Shekaru Takwas

 


Ya yi jawabin ne ga ba’adin iyalan Shahidan waki’ar a yayin da suka ziyarce shi a gidansa da ke Abuja, ranar Asabar 23/7/2022 (24/12/1443).

MUN SAMU RASHIN KYAKKYAWAR SADARWA

Assalamu alaikum wa Rahmatullahi Ta’ala wa barakatuhu.

Dafarko dai ina tsammanin akwai abin da ake ce mishi rashin kyakkyawar sadarwa, ni a yadda na dauka dama za a yi bikin tunawa da waki’ar Quds a nan Abuja ne, sai muka ce to tunda akwai lokaci za mu yi jawabi don a saka a karshen taron. In ya zama ba’adinsu (iyalan Shahidan) sai su zo, sai a yi musu bayani, sai ya zama maganar ce za ta zama ta ranar karshe din. To sai yanzu ne nake fahimtar cewa ashe ma dama taron ba a nan Abuja za a yi ba. 

Ashe ana Zariya ne, yau ne musamman aka taso don a zo nan. Kuma sai ya zama abin bakin ciki an samu matsala a hanya, an samu hatsarin mota, har ya zama yanzu wasu suna kwance a asibiti, to kuma wasu har da karaya, gasu nan sun tattago sun zo, to Allah ya sauwake dai. Da ace duk dama suna nan din ne da ya fi mana sauki, haka mu muka dauka. 

HATTA A BIRNIN DA QUDS TAKE BA A BUDEWA MUTANE WUTA RANAR QUDS

To, waki’ar Quds shekara takwas da suka wuce, wanda maganar da na yi na lokacin Quds na bana a karshen Ramadan, na fadi wata magana nake cewa wannan Ramadan din (ma) Juma’ar karshe ta fado ranar 28, wanda ya zama shekara takwas da suka wuce haka ta fado ranar 28 ga watan. 

To rannan ne kuma wadannan mutanen suka yi aika-aikar da suka yi. Aka yi taron Quds a ko ina a Duniya lafiya lau, aka yi a birane sama da 700 a duniya, amma labari sai ya nuna babu inda aka yi harbi sai a waje guda, shine a Zariya. Inda suka bude wuta suka kashe kimanin mutum 34.

To, wanda yake wani abu ne mai ban al’ajabi, don mutum babu yadda za a yi ya sauwala tunaninsa kan cewa wasu mutane sun fito suna cewa muna goyon bayan al’ummar Palasdinu wadanda ake zalunta. Sai kai kuma nan wanda yake hatta a can inda ake zaluntar Palasdinawan ba su taba tunanin ana wannan su bude musu wuta ba. Hatta a nan birnin Quds, idan ana wannan ranar Quds din basu tunanin su bude musu wuta.

Amma a nan wane irin tunani ne suke da shi wanda yake bani tsammanin ma suna tunanin, su kawai abin da ransu ke sauwala musu shine babu wani abu illa kawai bindiga a hannun Dan Bindiga, sa’awa’un Dan Sanda ne ko Soja ne shi bindigarsa ta kisan kai ne. Shi kawai abin da ya daukawa kansa ma bindigarsa ta kisan kai ne. kuma ba wanda zai ce masa komai ma idan ya yi kisan kai, bil-hasali ma goyon bayansa za a yi. 

Har ma duk wanda aka ba bindiga, wanda wannan karon ma har da irin su Custom, suma bindigarsu na harbe mutane ne. Haka kuma duk wani wanda aka ba bindiga iri daya kamar na ‘yan bindiga suma (kashe mutane suke).

Nake cewa hatta ‘yan fashi an san cewa ba suna harbi ne don su yi kisa ba, su kan nuna makami ne domin a basu dukiya, suna ba da tsoro ne da makami, idan ka ga dan fashi ya yi harbi to waje ya kure masa ne, yana ganin kamar asirinsa zai tonu ne, ko kuma su wadanda yake tsare su din yana ganin suma suna da makami irin nasa za su harbe shi, amma in ma tun farko ya san suna da makami ba zai ma fara ba.

To amma abin mamaki yanzu kawai sai ka ga an kawo mutane sun tsare hanya sun karkashe mutane kawai babu wani dalili. Ko su je gari su kashe mutane, ba wani dalili. To wannan wata irin musiba da ta auko mana a wannan al’umma da muka samu kanmu kenan.

IDAN MUKA BIYE TA AZZALUMAI KO SALLAH DA ADDU’A SAI SUN HANA MU

To ala ayyi halin, wasu mutane suna cewa wai to meye maganin wannan abin? Muna cewa to tuntuni dama mu ake mana, mu kadai ake ma. Wadansu suna ganin ma abin da ake mana din daidai ne. To yanzu kowa ake yi wa. 

Tun a wancan lokacin in ana cewa wai meye maganin wannan abin da suke mana, nakan ce to su abin da suke cewa shine ko dai ku dena abin da kuke yi ko kuma mu kashe ku. Abin da suka ce mana kenan, ko ku dena abin da kuke yi ko mu kashe ku. To kuma muna ganin babu iyaka da irin wannan barazana, nan gaba za su iya cewa ko sallah ba za ku yi ba, in kuka yi sallah za mu kashe ku.

Don sun rika mana haka, duk taro suna zuwa su bude mana wuta, hatta taron janaza suna zuwa da bindiga, hatta taron daurin aure sukan zo da bindiga, hatta walima in ana yi su kan zo da bindigoginsu suce a tashi idan ba haka ba za su bude wuta. Saboda haka taron daurin aure, taron jana’iza, da taron walima, duk ba ruwansu kawai, su dai kawai kowane taro ance wai su zo su kashe mu ne, ko ma me muke yi.

To kaga idan za mu fasa, to ranar da muka taru muna addu’a fa, me za su yi? Kawai za su zo su yi kisa ne, suce addu’ar mene? Ai ma an je addu’a a Darur Rahma suka zo da bindiga suka ce a tashi kawai. Ana cewa a karanta Qulhuwallahu, a karanta kaza da kaza, sai wani soja yana cewa dama ance mana su mushirikai ne. Sai wani soja dan uwansa yace masa kai sakarai ne, baka ji suna cewa a karanta Ayatul Kursiyyu ba? Yasu-yasu. Wai ana addu’a ne fa, wai amma wai ana bautawa wani ne ba Allah ba. Daga karshe suka ce a tashi kawai idan ba haka ba za su bude wuta. Aka ce ai addu’a ake yi. Suka ce a tashi kawai! 

Kaga idan addu’a ma za su bude masa wuta, to nan gaba idan suka zo ana sallar Juma’a fa ko na Idi, me za su mishi? Shima sai su bude wutan kenan. Ko kuma ma ‘Khamsu salawat’, shima sai su bude wutan.

Don ta kai ma akwai lokacin da in aka yi mafarkin cewa wata rana za a samu Hukuma tace kar a yi sallah, za a ce ba zai yiwu ba. To wannan karon sun yi haka nan, suka ce sun hana jam’i, duk suka rufe masallatai. Duk wani limamin da ya yi sallah sai a je a dauki hoto a kira shi a gaban Gwamna.

Akwai wani liman da aka kira shi gaban Gwamna, aka ce masa ka yi sallah. Yace a’a ranka shi dade ban yi ba. Sai aka dauko, ashe wai akwai ‘yan rahoto, da suka nuna masa hoto sai yace a yi hakuri ba zai sake ba. 

Sai ya zama wadanda suka je za su yi sallah, sai liman ya kulle masallacin sai dai su yi a barandan masallacin su watse, amma banda liman, saboda yana jin tsoro, saboda za a kama shi. Haka aka yi kwanakin da suka ce ana Corona din nan, ko ina ana sallah, amma a wani waje an hana sallah. To kaga da ace mune ma za mu yi sallah din, mu namu ma shikenan ba sai an ce a kira liman din ba, za a je ne a bude wuta kawai.

To har ma ta kai ma ga an yi zaman makoki na Ashura a cikin gida, ba a waje ba, kuma suka balle suka shiga gidan suka bude wuta suka kashe mutum uku a Kaduna. Zaman makoki na Ashura, ranar uku ga wata, an yi ranar farko da rana na biyu, rana ta uku kawai suka balla suka shiga gidan, to ina ruwanka da gidan mutum? 

Kuma zaman makoki a kan zauna ne mutum daya yana maganar abin da ya faru sauran mutane suna sauraro, masu sauraron nan suna iya zama kowa, kowa ma yana iya zuwa ya saurara, har da wanda yake ba Musulmi ba ma yana iya zuwa ya saurara, tunda ana magana ne. Mutum daya kuma ke magana saura suna sauraro, amma suka je suka bude wuta, kuma suka ga abin da suka yi din daidai ne.

To, wannan al’ummar da muke zaune a ciki kenan, wadanda suke ganin ko dai ku daina abin da kuke yi ko mu kashe ku. To me za mu yi? Za mu ce mun fasa ne? Sai muka ce to za mu yi, ku kuma kar ku fasa kisan. Dadin abin mai kisa shima yana mutuwa, ba yana rayuwa bane. Sannan kuma akwai karshe watan-watarana ba zai yi kisan ba.

Za mu cigaba.

— Cibiyar Wallafa Da Yada Ayyukan Shaikh Zakzaky (H).

No comments

Powered by Blogger.