Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar Da Sabon Tsarin Ci Gaban Zamfara Na Shekaru 10
Gwamna Dauda Lawal ya ƙaddamar da sabon Tsarin Ci Gaban Jihar Zamfara na 2025 zuwa 2034, wani tsari mai dogon zango da aka gina bisa bincike, bayanai, da tattaunawa da ƙwararru domin sake fasalin jihar a shekaru goma masu zuwa. An gabatar da shirin ne a sakateriyar JB Yakubu da ke Gusau a ranar Juma’a,…
TARON IILM NA 35: Yadda CBN ya gudanar da taron Kwamitin Gudanarwar Manyan Bankunan Ƙasashe Takwas
Ashafa Murnai Barkiya A ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Olayemi Cardoso, CBN ya gudanar da taron Kwamitin Gudanarwa na 35 na manyan bankunan duniya guda takwas, wato International Islamic Liquidity Management Corporation (IILM) a karon farko a Nijeriya, a Hedikwatar CBN da ke Abuja. Wannan taron dai ya yi daidai da wa’adin Gwamna…
Shugaba Tinubu ya rantsar da Janar Christopher Musa a matsayin sabon ministan tsaro
Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya rantsar da tsohon Babban Hafsan Tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa (ritaya), a matsayin Ministan Tsaro na ƙasar, a wani taro da aka gudanar a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja a ranar Alhamis. Rantsarwar ta biyo bayan murabus ɗin Alhaji Mohammed Badaru Abubakar a ranar 1 ga Disamba, wanda ya…
Gwamna Lawal Ya Gabatar da Kasafin Naira Biliyan 861 Ga Majalisar Dokokin Jihar Zamfara
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya gabatar da ƙudirin kasafin kuɗi na shekarar 2026 mai darajar Naira Biliyan 861 ga Majalisar Dokokin Jihar, inda ya bayyana shi a matsayin taswirar sauyi da kuma shaida cewa Zamfara na kan hanyarta ta tashi tsaye da ƙarfi. An gabatar da kasafin ne a ranar Alhamis a birnin Gusau….
Majalisar Dattawa ta tabbatar da tsohon Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, a matsayin Ministan Tsaro
Majalisar Dattawa ta tabbatar da tsohon Babban Hafsan Tsaro na Najeriya, Janar Christopher Musa (mai ritaya), a matsayin sabon Ministan Tsaro na ƙasar. An tabbatar da shi ne ranar Laraba ta hanyar kuri’ar murya, bayan zaman tantancewa da ’yan majalisar suka gudanar a zauren su na Kwamitin da ya haɗa kowa da kowa, inda suka…
CBN ya ƙara yawan kuɗin da za a iya cira daga ATM zuwa N100,000 a kullum
Ashafa Murnai Barkiya Bayanai daga Babban Bankin Najeriya (CBN) sun tabbatar da cewa an ƙara adadin kuɗin da za a iya cira ta hanyar amfani da katin ATM zuwa Naira dubu 100 a kowace rana. Sabuwar dokar ta ƙara adadin kuɗin da za a iya cira daga dukkan hanyoyin biyan kuɗi zuwa N500,000 a kowane…
Bincike Ya Nuna Cewa Ƙungiyar Da Ta Zargi Gwamna Lawal Da Yi Wa ’Yan Bindiga Afuwa Ta Bogi Ce
An gano cewa zargin da ake yaɗawa cewa Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yi afuwa tare da sakin ‘yan bindiga da aka yanke wa hukunci ba shi da tushe kwata-kwata, bayan cikakken bincike da jaridar PremiumTimes ta gudanar kan batun da ya tayar da ƙura a kafafen yaɗa labarai. A ranar 28 ga Nuwamban…
CBN Ya Umarci Bankuna Su Mayar Wa Waɗanda Aka Yi Wa Zambar ‘APP’ Kuɗin Da Suka Yi Asara Cikin Awanni 48
Ashafa Murnai Barkiya A wani sabon tsarin ƙara kare haƙƙin kwastomomi masu hulɗa da bankuna da kuma kare su daga ɗibga asara, Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya fitar da wani sabon umarni da ke wajabta wa bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi su mayar wa waɗanda suka faɗa cikin zambar ‘Authorised Push Payment’ (APP) kuɗin su…
Gwamnatin Tarayya Ta Ce Babu Musguna Wa ’Yan Jarida a Mulkin Tinubu
Gwamnatin Tarayya ta jaddada cewa gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta himmatu wajen tabbatar da ‘yancin ‘yan jarida, kare dimokiraɗiyya, da tabbatar da tsaro a fagen yaɗa labarai a Nijeriya. Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana hakan a Taron Shekara-shekara na Cibiyar ‘Yan Jarida ta Duniya…
Shugaba Tinubu ya mika sunan Janar Christopher Musa domin zama Ministan Tsaro
Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya mika sunan tsohon Babban Hafsan Tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa, ga majalisar dattawa domin tabbatar da shi a matsayin sabon Ministan Tsaro, bayan murabus din Alhaji Mohammed Badaru Abubakar. A wata wasika da ya aika wa Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, Shugaba Tinubu ya ce nadin Janar Musa ya…
